Wednesday, 22 May 2019

Tauraron dan wasa ya zabi komawa Real Madrid maimakon Barcelona saboda Messi

Tauraron dan wasan Eintracht Frankfurt, Luka Jovic da ya samu nasara sosai a gasar Bundesliga inda ya zura kwallaye 27 hakan yasa manyan kungiyoyin turai suka yi caa akan neman sayenshi. Real Madrid da Barcelona ne a gaba-gaba wajan sayen dan wasan saidai ya ki yadda da Barca saboda Messi.Frankfurt  na neman fan miliyan 52 akan Jovic wanda ya taimaka mata taje wasan kusa da na karshe na gasar Europa inda Chelsea ta cire su a bugun daga kai sai gola.

Madrid na nemam Jovic dan shekaru 21 a matsayin wanda zai rika taimakawa Benzema a gaba ko kuma ya zamana shi kadai.

Hakanan Barcelona na neman dan wasan a matsayin wanda zai maye Luis Suarez wanda ya fara gajiya, saidai Jovic ba ya son zuwa Barca saboda ganin cewa ba zai samu damar yin wasa akai-akai ba ko kumama ba za'a rika fara wasa dashi ba a cikin 11 farko, kasancewar fifikon da kungiyar ta ke baiwa Messi, ga Suarez din ga kuma maganar sayen tauraron Atletico Madrid, Griezmann.

Abin jira a gani shine idan Barca zata iya canjawa matashin dan wasan ra'ayi akan zabarta maikaon Madrid.

1 comment:

  1. To shi jovic meyasa yayi haka, ko baison buga wasa da messi ne

    ReplyDelete