Monday, 20 May 2019

Tauraron dan wasan Madrid na son komawa Barcelona dan yin wasa da Messi


Wasu rahotanni na bayyana cewa tauraron dan kwallon Real Madrid, Isco Alarcon na shirin barin kungiyar zuwa babbar abokiyar takarar ta, watau Barcelona.

Zidane ya riga ya nunawa, Gareth Bale, Dani Ceballos da Marcos Llorente cewa basa cikin wadanda yake son yin wasa dasu a kungiyar, kuma ana ganin Isco da karin wasu 'yan wasan na kan hanyarsu ta barin Madrid.

A yayin da ya sake sakawa Madrid hannu a kwantirakinshi shugaban Madrid, yawa Isco alkawarin karin albashi, alkawarin da ba'a cika mai ba, wannan na daga cikin abinda ake hasashen zai tunzura dan wasan ya bar Madrid.

Ana dai ganin da wuya Madrid ta sayarwa da Barca Isco sannan ana alakanta dan wasan da komawa kungiyar Manchester City.

No comments:

Post a Comment