Monday, 20 May 2019

Trump ya goyi bayan dokar haramta zubar da ciki a Amurka


media
Karon farko bayan daukar tsawon lokaci ana takaddama kan dokar haramta zubar da ciki a wasu jihohin Amurka, shugaban kasar Donald Trump ya fito ya goyi bayan dokar musamman ga matan da aka yiwa Fyade ko bukatar zubar da cikin ta taso saboda lalura ta rashin lafiya.

Tuni dai dubban jama’a suka tsunduma zanga-zanga da matakin, galibi a jihar Alabama wadda ba ta yi sassauci kan nau’in zubar da cikin ba, inda sabuwar dokar ta haramta zubar da cikin ta kowacce fuska.
Shima dai shugaban kasar, wanda wannan ne karon farko ta tsoma baki game da takaddama kan sabuwar dokar y ace, baya goyon bayan zubar da ciki face ga matan da aka yiwa Fyade ko lalura ta rashin lafiya ta bukaci hakan.
Tawagar masu maraba da matakin a jihar ta Alama inda a nan ne lamarin ya fi tsananta ta bukaci gaggauta tabbatar da dokar ba tare da barin wani gurbin yi mata kwaskwarima ba, yayinda wadanda ke adawa da dokar suka nemi daukaka kara.
Matukar dai ana bukatar dorewar dokar akwai bukatar ta isa gaban kotun koli, inda a nan ne za ayi mata geji ta yadda babu wata kotu da za ta yiwa dokar kwaskwarima.Yanzu haka dai akwai Karin jihohin kasar ta Amurka 16 da ke bukatar ganin gwamnatocinsu sun bi sahun Alabama wajen haramta zubar da cikin ta kowacce fuska.
Duk da kasancewar batun zubar da ciki lamari mai sarkakiya a Amurka, Donald Trump ya ce ya ki jinin bayar da damar zubar da ciki babu gaira babu dalili yana mai cewa akwai bukatar bai wa ‘yan tayin jarirai damar rayuwa.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment