Wednesday, 15 May 2019

Trump Ya Shiryawa Musulmi Bude-Baki a Fadarsa

Shugaban Amurka Donald Trump ya shirya wa jami'an diflomasiyyar kasashen da Musulmi suka fi rinjaye bude-baki a fadarsa ta White House.


Trump ya kwatanta liyafar wacce aka yi ranar Litinin a matsayin, “babbar karramawa gare shi” ta shirya bude-baki ga jakadun kasashen duniya da Musulmai sukafi yawa.

Ya bayyana watan Ramadana a matsayin lokacin jin- kai ga marasa karfi, kyautata danganta da kara kusantar iyalai da jama’a.

Trump ya yi magana akan abin da ya kira “matsananancin lokaci” musamman ga mabiya wasu addinai, har ya tabo zancen wasu hare-haren da aka kai kan cibiyoyin addinai na Musulmai, Kiristoci da Yahudawa a kasashen New Zealand, Sri Lanka da nan Amurka.
VOAhausa.


No comments:

Post a Comment