Wednesday, 15 May 2019

Tsakanin wani bawan Allah da yace Maza su auri matar da zata karfafa musu gwiwar kara aure dan raya sunna da wata budurwa


Wani bawan Allah ya bayar da shawara ga maza akan su auri matar da zata basu shawarar kara aure dan su cika sunna. Matar da zata ma baka shawarar irin abokiyar zamar da zaka kawo mata. Saidai amsar da wata ta bashi ta dauki hankula.
 
Wata baiwar Allah ta bashi amsar cewa, to ina ma ace mutum ya auri matar da zata taimaka mai wajan karatun Atayul Kursi da kuma tabbata yayi alwala kamin ya kwanta? Ta yanke maka farata duk Juma'a, ta karfafa maka ku karanta suratul Kahf tare, ta tasheka cikin dare ku yi sallah, ta tuna maka girmama iyayenka, da ziyarar marasa lafiya, da neman halal da sadaka. Inama ace ka samu irin wannan matar?

Wannan amsa tata ta dauki hankula sosai.

No comments:

Post a Comment