Saturday, 25 May 2019

Valencia ta doke Barcelona a wasan karshe na Copa del Reya duk da kokarin da Messi yayi: Saidai duk da haka Messin ya kafa tarihin da babu dan kwallon da ya taba kafawa

Kuma dai, Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sake gamuwa da wani mummunan rashin nasara a wasanta na karshe na kakar wasan 2018/19 inda suka yi rashin nasara a hannun Valencia da ci 2-1 a wasan karshe na daukar kofin Copa del Rey.'Yan wasan Valencia, Gameiro, da Rodrigo ne suka saka kwallaye biyu a ragar Barcelona tun a kamin a tafi hutun rabin lokaci, duk da cewa bayan dawowa daga hutun rabin lokacin, Messi ya saka kwallo daya amma Valencia ce ta yi nasara a wasan.
Messi dai ya kafa tarihi a wannan wasan inda ya zama dan kwallo na farko da ya ci kwallaye(7) a wasannin karshe shida na gasar Copa del Rey.

Kuma dadin dadawa, Wannan ne karin farko da aka ci Barcelona kwallaye biyu tun kamin a je hutun rabin lokaci a wasan karshe na Copa del Rey cikin shekaru 67 da suka gabata, hakan ya farune a shekarar 1952 wanda kuma Valencia ce dai ta wa Barca wancan abin kunyar a wancan lokaci.

Rashin nasara a wasan kusa dana karshe na gasar cin kofin Champions League da kuma wasan karshe na gasar Copa del Rey ya saka tantama akan ko me horas da kungiyar ta Barcelona, Ernesto Valverde, zai ci gaba da zama a kungiyar?

Sanan Messi ya fada cewa idan suka yi rashin nasara a wannan wasan zasu shiga yanayi mafi muni da yafi na Liverpool.

No comments:

Post a Comment