Monday, 20 May 2019

WASIYYA BAKWAI DA ANNABI SAW YA YIWA ABU ZARRI R A.

AL-IMAM AHMAD BN HAMBALI R, YA RUWAITO HADITH،(20906)  WANDA SHAIKH ALBANI YA INGANTASHI, A CIKIN SILSILATUS SAHIHAH (2166). DAGA ABU ZARRI RA YACE :  
MANZON ALLAH SAW YAYI MINI WASIYYA DA ABUBUWA BAKWAI: 
NA DAYA,  NA SO TALAKAWA KUMA NA DINKA KUSANTAR SU.( KAUNAR SU DA TAIMAKON SU.) 


NA BIYU,  NA DINKA DUBAN NA KASA DA NI, KADA NA DINKA DUBA NA SAMA DA NI, (DOMIN MAI DUBAN NA SAMA DA SHI BA ZAI YI GODIYA BA.) 
NA UKU,  NA DINKA SADA ZUMUNTA KO DA DANGINA  SUN YANKE TA. ( IDAN BASA ZUWA GURI NA NA NA DINGA ZUWA GURIN SU DOMIN ALLAH.) 
NA HUDU,  KADA NA ROKI KOWA KOMAI. ( DOMIN ROKO DA BARA YANA ZUBAR DA MUTUNCIN MUTUM.) 
NA BIYAR,  YA UMARCENI NA FADI GASKIYA KOMAI DACINTA. (DOMIN FADAR GASKIYA A GABAN WANDA AKE TSORONSA KUMA AKE KWADAYIN ABIN HANNUN SA YANA DA WAHALA.) 
NA SHIDA,  YA UMARCENI KADA NA JI TSORAN ZARGIN MAI ZARGI. (DOMIN WANI LOKACI TSORAN ZARGI YANA HANA MUTUM BAYYANA ABINDA YA TABBATAR SHINE GASKIYA) 
NA BAKWAI, YA UMARCENI NA YAWAITA FADAR LA HAULA WALA KUWWATA ILLA BILLAHI

(DOMIN WANNAN KALMA TASKA CE DAGA A GIDAN ALJANNAH. 

ALLAH YA BAMU AIKI DA WANNAN WASIYYA. 
لا حول ولا قوة الا بالله
Malam Aminu Ibrahim Daurawa.


No comments:

Post a Comment