Sunday, 5 May 2019

Wata kungiya na neman sayen Ronaldo da Messi su buga mata wasa


Rahotanni da zafizafi na nuna cewa wata kungiyar kwallon kafa na shirin hada manyan 'yan wasan kwallon kafa na Duniya biyu, watau Cristiano Ronaldo da Lionel Messi dan su yi mata wasa a lokaci guda, wannan wani abune da dubban masoya kwallon kafa ke mafarkin ganin ya tabbata, to saidai ko hakan zata yiyu kuwa?

Tsohon tauraron dan kwallon kafa wanda kuma yanzu shine shugaban kungiyar Inter Miami dake Florida kasar Amurka, David Beckham na son ganin cewa ya hada Messi da Ronaldo a wannan kungiya tashi.

Shafin kwarmato labaran kwallo na Diario Gol ya ruwaito cewa Beckham na da mafarkin ganin ya siyo Lionel Messi da Ronaldo su buga mai wasa dan ya jawo ra'ayin masoya kwallon kafa musamman acan Amurkar wajan kallon wasannin kungiyar tashi.

Yana son yayi hakane kamin shekarar 2021 wanda a lokacinne kungiyar zata kammala ginin sabon filin wasanta da take kan ginawa, burin Beckham shine wasa na faro da Inter Miami zata yi a filin wasan bayan an kammala gininshi ya kasance da Messi da Ronaldo ne.

A kwanakin baya, Ronaldo ya taba bayyana sha'awar bugawa kungiyar ta Inter Miami wasa kamin yayi ritaya daga buga kwallon kafa, hakanan shima Messi bashi da burin barin Barcelona zuwa wata kungiya a nahiyar turai, saidai watakila wajan Nahiyar turai, kuma Inter Miami a Amurka take.

Sannan idan Beckham zai kawo Messi da Ronaldo to zai ya tanadi albashin da zai basu na fan miliyan 75 duk shekara kowannensu.

Ko Beckham zai iya yin wannan abu kuwa?

zadai mu jira mu gani.

No comments:

Post a Comment