Monday, 6 May 2019

Wata shahararriyar me saka hotunan batsa a yanar gizo tace ta daina har sai bayan Ramadana


Image result for cossy orjiakor pictures
Tauraruwar fina-finan kudu kuma mawakiya, Cossy Orjiakor da ta yi suna wajan saka hotunan batsa a shafukanta na yanar gizo ta amince da kiran da wani musulmi ya mata da ta dena saka hotunan batsar har sai bayan watan Azumin Ramadana.

Cossy Orjiakor ce da kanta ta saka sakon da musulmin ya aike mata ta shafinta na sada zumunta inda yace, bayan gaisuwa, ina baki hakuri idan abinda an fada zai bata miki rai, bani da nufin musguna miki, ina son in yi wani roko a gareki a madadina da sauran 'yan uwana musulmai dake bibiyarki. Za ki iya daina saka hotunan batsa saboda watan azumin Ramadana da za'a fara gobe, ya karkare da cewa mutum tara yake be cika goma ba.

Ita kuma ta amince inda tace zata daina.

No comments:

Post a Comment