Sunday, 19 May 2019

Ya kamata a ware rana daya duk wata ta yin kuka a Najeriya>>Tsohon gwamnan Osun

Tsohon gwamnan jihar Osun, Ogbeni Rauf Aregbesola ya bukaci cewa ya kamata a ware rana daya a kowane wata a Najeriya dan a rika zabga kuka saboda matsalar da kasar take ciki.Aregbesola ya bayyana hakane a jihar Legas wajan murnar zagayowar ranar haihuwar wani jigo a jam'iyyar APC, da yake magana akan kudin shigar da Najeriya ke samu da kuma yawan al'ummar kasar, Aregbesola yace, ba mu tunawa cewa Najeriya matalauciyar kasace. Idan mu ka yi tsam ya kamata mu ware rana daya ta yin kuka duk wata.

Idan ba mu yi abinda ya kamata ba wajan rufawa kanmu asiri ta zamu ci gaba da kasancewa a cikin talauci. Ya bayar da misalin cewa a shekarar 2017, kasar Brazil tana da yawan mutane kimanin miliyan 200, kusan kamar yawan mutanen Najeriya kenan.

A waccan shekarar Brazil ta samu kudin shiga da suka kai dala biliyan 600 sannan tana da kasafin kudi da ya kai dala biliyan 700. A waccan shekarar dai Najeriya ta samu kudin shiga da suka kai dala biliyan 13 sannan ta yi kasafin kudi na dala biliyan 23, kamar yanda The Nation ta ruwaito.

Aregbesola ya tambayi cewa shin kasashen biyu daidai suke?

Ya kara da cewa OPEC ta baiwa Najeriya damar ta rika fitar da danyen mai ganga miliyan 2 kullun wanda bama a samun ya kai hakan. Yace koda ace ana samun ganga miliyan 2 din a kullun kuma ana sayar da kowace ganga akan dala 100 to za'a samu kudin shiga dala miliyan 200 ne.

Yace idan ka rabawa mutane miliyan 200 dala miliyan 200 kowannensu zai samu dala 1 ne. Ya kara da cewa to ya kamata mu fara amfani da tazarar haihuwa dan magance yawan mutanem kasarnan. Idan bamu yi maganin wannan ba to muna da babbar matsala a gaban mu. Yace kuma ya kamata duk wani me karfi a jika ya zamana yana da aikin yi.


No comments:

Post a Comment