Friday, 10 May 2019

'Yan bindiga sun tilasta wa jama'ar Shinkafi kwana a daji


media
‘Yan bindiga sun tilasta wa jama’ar Karamar Hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara a Najeriya kwana a cikin daji sakamakon farmakin da suka kawo musu a tsakiyar daren da ya gabata, inda suka yi awon gaba da akalla mutane 40 da suka hada da ‘yan kasar Ghana.

Jama’ar yankin sun shaida wa sashen hausa na RFI cewa, sun yi ta kabbara da kiran salla da nufin samun kwarin guiwar tunkarar ‘yan bindigar.
Dr. Sulaiman Shu’aibu Shinkafi, Sarkin Shanun Shinkafi ya bayyana takaicinsa kan yadda jami’an sojoji suka ki kawo musu dauki a yayin hare-haren har sai da 'yan bindigar suka ci karensu babu babbaka.
A cewarsa, daga yanzu babu wani sauran kwarin guiwa da suke da shi akan sojojin Najeriya domin kuwa sun gaza gudanar da ayyukansu na kare rayukan al’ummar yankin.
Dr. Shinkafi ya kara da cewa, daga yanzu za su ci gaba da dogara da kansu wajen samar wa kansu kariya daga ‘yan bindigar saboda jami’an tsaron sun gaza.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment