Saturday, 11 May 2019

'Yan siyasa basu da banbanci da karuwai>>Dr. Ahmad Gumi


Shehin malamin addinin Islama, Sheikh, Dr. Ahmad Gumi ya kwatanta 'yan siyasa da cewa basu da banbanci da Karuwai, musamman masu tsilla-tsilla daga wannan jam'iyyar zuwa waccan.

Dr. Gumi ya bayyana haka ne a yayin da aka mai wata tambaya akan ko su malaman addini nada karfin fada aji a wajan 'yan siyasa musulmai? sai ya kada baki yace, mafi yawancin 'yan siyasa basu da alkibla, shiyasa zaka ga suna tsilla-tsilla daga wannan jam'iyya zuwa waccan, kamar yanda Leadership ta ruwaito.

Yace malamai na bayar da fatawa ga 'yan siyasa, wasu daga ciki na dauka wasu kuwa basa dauka bisa dalilan da su kadai suka sani.

Yayi wannan jawabine wajan wani taro na musamman da aka yi a garin Kaduna.

No comments:

Post a Comment