Saturday, 11 May 2019

Yanda aka jibge jami'an tsaro a fadar sarkin Kano


Wasu rahotanni daga jihar Kano na cewa an jibge jami'an tsaro a fadar sarkin Kanon, Muhammad Sanusi na II da gidajen wasu ma'aikatan fadar.

Motocin Hilux ne guda 10 suka kai jami'an tsaron fadar da aka girke a kofar kudu, kamar yanda Daily Trust ta ruwaito. Hakanan akwai wasu karin goma da aka jibge a kofar gidan shugaban ma'aikatan fadar, Malam Muhammad Sanusi dake kan titin Iyaka.

Hakanan an jibge karin wasu goma a babbar kofar shiga fadar gwamnatin jihar Kano. Sannan an jibge wasu karin jami'an tsaron a kofar sakateriyar jihar Kanon. Kakakin 'yansandan jihar ta Kano, DSP Haruna Abdullahi ya bayyana cewa besan da wannan aikin na 'yansanda ba amma da zarar ya samu karin bayani zai gayawa manema labaran.

No comments:

Post a Comment