Wednesday, 1 May 2019

Yanda aka kawo mana hari amma sojoji sukaki kawo mana dauki duk da mun kirasu>>Sarkun Bungudu


Sarkin Bungudu, Alhaji Hassan Attahiru ya bayyana cewa, hare-haren 'yan ta'adda a jihar Zamfara baya raguwa duk da yakin da sojojin kasarnan ke yi dasu.

Sarkin ya bayar da labarin yanda a ranar Asabar 'yan ta'addar suka kaiwa yankinshi hari, kuma shugaban karamar hukumar ya kira shugaban sojojin dake yaki da 'yan ta'addar amma  suka share suka ki zuwa.

Sarkin yace, mutane 15 'yan ta'addar suka kashe, sannan abu mafi muni shine shugaban karamar hukumarmu ya kira shugaban sojin sama dan su kawo mana dauki, amma abinda aka gayamai shine, be kamata in dauki wayarka ba tunda kun zabi ku kunyatar damu. Sarkin yace da shugaban karamar hukumar ya kawo mai maganar ya dauki waya ya kira shugaban sojin har sau uku amma be dauka ba kuma har zuwa litinin be kirashi ba, kamar yanda Punch ta ruwaito.

Sarkin ya kara da cewa, bamuce basa yin komai ba amma maganar gaskiya sama-sama suke yaki da 'yan ta'addar basa binsu har maboyarsu.

Da yake mayar da martani akan wannan lamari, me magana da yawun rundunar Operation Sharan Daji, Maj. Clement Abiade ya bayyana cewa be samu labarin sojin dake Zamfara dan baiwa mutane kariya sun yi watsi dasu a lokacin da jama'ar ke bukatarsu, ya bukaci mutane da idan irin wannan abu ya faru su rika kiran fiye da mutum daya a rundunar sojin dan duk suna da lambobinsu.

No comments:

Post a Comment