Monday, 6 May 2019

'Yanda dan uwana da masu garkuwa da mutane suka yi artabu: Ya kashe daya ya jiwa daya rauni'


Wani bawan Allah me amfani da shafin Twitter ya dauki hankula bayan da ya bayar da labarin cewa, masu garkuwa da mutane dan neman kudin fasa sun kaiwa gidan dan uwanshi dake Kaduna hari, yace Allah ya taimaki dan uwan nashi nada bindiga me lasi.

Nan suka yi bata kashi, ya kashe daya, ya jiwa daya rauni.

Ya karkare da cewa muna cikin matsala. mutum ya zamana yana cikin shiri a ko da yaushe.

No comments:

Post a Comment