Wednesday, 22 May 2019

Yanda idon Mbappe ya rufe akan komawa Real Madrid

Me horas da kungiyar Arsenal,Unai Emery ya bayyana yanda yasha fama da Kylian Mbappe lokacin yana PSG a akan komawa Kungiyar Real Madrid da yaso yi.Da yake baiwa El Laguero labari, Emery ya bayyana cewa, yayi magana da Mbappe da mahaifinshi a wancan lokacin duk dan kokarin ganin ya shawo kanshi kada ya bar PSG zuwa Real Madrid, yace amma lokacin idonshi ya rufe.

Yace har tallar komawa Barcelona aka kawowa Mbappe amma yaki yace shi dai Madrid yake son komawa.

Yace da kyar da jibin goshi suka shawo kan matashin dan wasan inda saida ya bukaci wasu kudi kuma kungiyar ta bashi sannan ya amince ya zauna.

Mbappe dai ya nuna takaici da rashin samun damar buga gasar Champions League na kungiyar tashi.

No comments:

Post a Comment