Wednesday, 22 May 2019

ZA A HARAMTA AMFANI DA LEDA A NIJERIYA

Kwamitin da ke kula da muhalli na majalisar wakilai ta tarayya ya amince da kudirin da ya haramta amfani, sarrafawa tare da shigo da jakar leda domin amfanin yau da kullum, musamman ma gurin siyayyar kayan cefene da zuba 'yan kayayyaki. 


'Yan majalisar dokokin sun rattaba wa kudirin haramta amfani da jakar ledar hannun da kyakkyawar niyyar kare muhalli daga matsalolin da leda ke jawowa ta hanyar cushe gurare da magudanar ruwa.

Kudirin ya umarci masu sayar da kayayyaki da su zuba wa abokan kasuwancinsu kayan da suka saya a cikin jakar takarda. Gaza hakan kuma laifi ne. 

Ya kara kuma da fadin cewa shi ma wanda ya sarrafa ledar domin sayarwa ya aikata laifi.

A dangane da kudirin, dukkan wanda aka kama da karya dokar zai biya tarar naira 500,000, ko kuma zaman gidan kaso na tsawon wata uku, ko kuma a hade tarar da kuma zaman gidan kaso.

Su kuma masana'antu za su biya tarar naira miliyan biyar idan aka kama su suna sarrafawa domin sayarwa. 

Tuni dama kasashen da suka ci gaba suka haramta amfani da leda a kasashensu, inda suka zabi amfani da jakar takarda sakamakon hadarinta ga muhalli da lafiyar mutane.


No comments:

Post a Comment