Sunday, 19 May 2019

Zidane yayi barazanar ajiye aikin horas da 'yan wasan Real Madrid

Me horas da kungiyar Real Madrid, Zinedine Zidane ya aikawa mahukuntan kungiyar gargadin cewa idan ba za'a bashi cikakken ikon zabar 'yan wasan da zai rika buga wasa dasu ba to zai ajiye aikinshi.Zidane yayi maganane akan zaban golan da zai rika buga wasa dashi a matsayin zabin farko, yace ba zai rika amfani da yawan kudin da aka siyo dan wasa wajan sakashi a wasanshi ba, yace maganar sayen 'yan wasa, ya yadda zasu hada kai da wanda keda hakkin hakan su yi aiki tare.

Amma maganar wa da wa zasu shiga fili su buga wasa wannan shawararshi ce da ya kamata ace shi kadaine zai yanke, idan kuma ya rasa haka to zai ajiye aikin.

No comments:

Post a Comment