Friday, 14 June 2019

A daina cemin matar shugaban kasa, daga yanzu First Lady za'a rika kirana>>A'isha Buhari

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya A'isha Buhari ta bukaci cewa daga yanzu a daina kiranta da uwargidan shugaban kasa, a rika ce mata First Lady.A'isha Buhari ta bukaci hakane a jiya, Alhamis wajan taron karrama matan gwamnoni masu ci da wanda suka sauka daga mulki da ya wakana a dakin taro na fadar shugaban kasa.

A'isha Buhari ta bayyana cewa a lokacin da aka sake zabar mijinta a matsayin shugaban kasa a karo na biyu, ta bukaci da a rika kiranta da matar shugaban kasa. Saidai ta lura da cewa hakan ya jawo rudani tsakanin matan gwamnoni inda wasu suka rika tunanin suma a kirasu da matar gwamna ko kuwa First Lady ta jiha?

A'isha tace domin kawar da wancan rudani ne yasa ta ce kawai daga yanzu a daina ce mata matar shugaban kasa, a rika kiranta da First Lady. Ta kuma nemi afuwar matan gwamnonin akan hakan, kamar yanda kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito.

No comments:

Post a Comment