Pages

Wednesday 26 June 2019

A karshe dai gwamnati ta saki kudin alawus din Super Eagles

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan wasan Najeriya na Super Eagles dake wakiltar kasar a gasar cin kofin nahiyar Afrika da ake buga a kasar Egypt sun janye fushin da suka yi kan kin biyansu alawus-alawus dinsu da suke bin hukumar kwallon kafa ta NFF bashi.



Rahoton yace NFF tace gwamnatin tarayya bata sakar mata kudin na 'yan kwallon ba, matsalar kudin sun zo a makarene shiyasa kuma yanzu tana kokarin ganin ta canja kudinne zuwa dalar Amurka a babban bankin Najeriya CBN kamin ta biya 'yan wasan.

NFF ta wa 'yan wasan alkawarin zata biyasu nan da karshen wannan makon.



Wakilin NFF din ya bayyana cewa alawus din wasan da Super Eagles suka ci Burundi kawai suke bi amma ana biyansu kudin alawus din atisaye na dala 200 kowane dan wasa.

A jiyane dai labari ya watsu cewa, 'yan kwallon na Najeriya sun fara bore inda suka ki fitowa tattaunawa da 'yan jaridu da ake yi kamin fara wasa da kuma zuwa yin atisaye a Makare saboda kin biyansu alwus din da suke bi bashi da aka yi.

No comments:

Post a Comment