Saturday, 1 June 2019

A TAIMAKA A HADA SHUGABA BUHARI DA YAYANSA DA SUKE UBA DAYA

Jama'a wannan bawan Allah da kuke gani a hoto sunansa Idi Usman, amma amfi saninsa da sunan Baba Idi, yanzu haka yana da zama a wani gari mai suna Garin-Gabas dake karamar hukumar Hadejia jihar Jigawa, yana da shekaru 95 a duniya


Baba Idi jinin shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne, babansu daya da shugaba Muhammadu Buhari, Mahaifiya ce kowa da nasa, yana matsayin yaya ga shugaba Buhari

Yadda abin ya kasance shine: asalin Mahaifiyar Baba Idi 'yar garin Garin-Gabas ce, shekaru kusan dari 100 da suka gabata mahaifinta ya dauketa suka tafi garin Daura karatun Allo, anan ne mahaifin su shugaban kasa Muhammadu Buhari wato Malam Usmanu ya ganta kuma ya aureta tare da mahaifiyar babbar yayan su shugaba Buhari ana kiranta da suna 'Yar Dindi amma ta rasu

Mahaifin su shugaba Buhari yana da mata biyu a lokacin kafin ya auro mahaifiyar shugaba Buhari kenan, sai aka samu cikin Baba Idi, anan ne aurenta da mahaifin su shugaba Buhari ya mutu ta koma garinsu Garin-Gabas a Kasar Hadejia tana dauke da cikin Baba Idi kenan

Shi kuma mahaifin su shugaba Buhari wato Malam Usman sai ya sake yin wani aure, ya auri wacce ta haifi shugaba Buhari, shugaba Buhari bai shekara 4 ko 6 a duniya ba Mahaifin nasu Malam Usmanu ya rasu, Buhari sai ya tashi a hannun Mahaifiyarsa, lokacin ita kuma mahaifiyar Baba Idi ta jima da haifar Baba Idi a Garin-Gabas har ma ya girma ta kaishi makarantar Allo kafin mahaifiyar shugaba Buhari ta haifeshi a Daura

Kakan su shugaba Buhari wato wanda ya haifim Babansu 'ya'yansa uku ne, akwai;
1- Usman wanda yake shine mahaifin su shugaba Buhari da Baba Idi )
2- Abdullahi
3- Sarki Muhammad Bashari (Baban Sarkin Daura na yanzu wanda shugaba Buhari yake amfani da sunansa

Baba Idi bai taba sanin mahaifinsa ba, tunda Mahaifiyarsa ta kaishi makarantar Allo bai dawo gida ba sai kamar bayan shekaru 35, ya zo ya tarar da mahaifiyarsa ta rasu a nan garin Garin-Gabas kenan, shine sai ya fadawa '
Daga Datti Assallafiy 


No comments:

Post a Comment