Wednesday, 12 June 2019

A yanzu bamu da hujjar kin yiwa 'yan Najeriya aiki>>Shugaban APC

Shugaban jam'iyyar APC Adams Oshiomhole ya bayyana cewa a yanzu da jam'iyyar ta samu shuwagabannin da ta ke so suka zama masu jan ragamar majalisun tarayya biyu bata da hujjar kin yiwa 'yan Najeriya aiki.Oshiomhole ya bayyana hakane a jiya Talata bayan kammala zaben shuwagabannin majalisun tarayyar, na wakilai dana dattijai da aka yi wanda kuma duka 'yan takarar da jam'iyyar ta tsayar suka yi nasara.

Ya bayyana cewa irin farin cikin da yake ciki kamar na mace me cikine da ta haifi 'yan biyu, gashi sun samu shuwagabannin majalisar tarayya duka nasu. Ya kara da cewa sun yi kokarin magance aukuwar irin matsalar da aka samu a shekarar 2015 ne kuma sun yi nasara.

Yace a yanzu basu da wata hujjar kin yiwa 'yan Najeriya aiki kasancewar babu hujjar cewa majalisa na kawo musu cikasa, dolene yanzu su yi aiki ta bangaren tsaro da tattalin arziki da kuma inganta rayuwar Al'umma dan abinda 'ya  Najeriya suka sabesu akai kenan.

No comments:

Post a Comment