Tuesday, 11 June 2019

Ahmed Lawan ya zama shugaban majalisar dattawa

An bayyana Sanata Ahmed Lawan na jam'iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban majalisar dattawan Najeriya, inda ya samu kuri'a 79.


Ya kayar da mutum daya tilo da ya yi takara da shi, Sanata Ali Ndume daga jihar Borno, wanda ya samu kuri'a 28.

Hakan na nufin Sanata Lawan, wanda ke wakiltar Arewacin Yobe, ya yi nasara da tazarar kuri'a 51.

An kuma zabi Sanata Omo-Agege na jam'iyyar APC a matsayin mataimaki, inda ya doke Sanata Ike Ekweremadu na PDP.

Tuni Ali Ndume da Ekweremadu suka taya mutanen da suka kayar da su murna.

Zaben ya haifar da ce-ce-ku-ce musamman bayan da jam'iyyar APC ta nuna goyon bayanta ga takarar Ahmed Lawan.

Sannan ita kuma PDP ta goyi bayan Ali Ndume.

Sanatoci 107 suka kada kuri'a gaba daya a cikin 109.


Wane ne Ahmed Lawan
Sanata Ahmed Ibrahim Lawan, wanda ke wakiltar Arewacin Yobe, gogaggen dan majalisa ne wanda ya shafe shekara 20 a zauren majalisar tarayya.

An fara zabarsa ne zuwa majalisar tarayya a shekarar 1999, inda kuma ya kasance a can har zuwa shekarar 2007.

Ya shugabanci kwamitoci daban daban da suka hada da na ilimi da kuma ayyukan noma.

Dr Ahmed Lawan, wanda aka haifa a shekarar 1959 a jihar Yobe, inda kuma ya yi digiri na farko a jami'ar Maiduguri, kafin ya yi na biyu a Jami'ar Ahmadu Bello da kuma na uku a Burtaniya, ya zama Sanata a 2011.

Ya shugabanci kwamitoci daban daban, kuma ya zama mamba a kwamitin gyaran tsarin mulki na kasa.

An nada shi shugaban masu rinjaye bayan da aka sauke Sanata Ali Ndume a wani yanayi mai cike da rudani.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment