Tuesday, 11 June 2019

Akwai matsala a nasarar da Buhari ya samu>>Human Rights Watch

Hukumomi a Nijeriya sun fara mayar da bayani kan rahoton zaben shugaban kasar na baya-bayan nan da hukumar kare hakkin dan'adam ta Human Rights Watch ta fitar, inda ta ce nasarar shugaba Muhammadu Buhari na cike da rikita-rikitar siyasa.


Rahoton ya ce tun daga shekarar 2018 da aka fara yakin neman zabe ake ta samun tashin hankula a wasu sassan kasar, har zuwa lokacin da aka gudanar da zabe a watan Fabrairun 2019, kuma gwamnati ta gaza daukar matakan magance matsalar.

Human Rights Watch ta ce mutane fiye da 600 ne suka mutu sakamakon rikicin siyasa da hare-haren da mayakan Boko Haram sukai ta kai wa a shiyyar arewa maso gabashin Najeriyar a lokacin zaben.


Rahoton ya kuma zargi hatta sojoji da `yan sanda da hannu a cikin wasu kashe-kashen, ga kuma matsalar satar mutane dan neman kudin fansa da harin 'yan bindiga a shiyyar arewa maso yammacin kasar ita ma ta taka muhimmiyar rawa wajen dagula lissafi a lokacin zaben, a cewarta hukumar lamarin ya fi muni a jihohin Kano da Rivers.

Sai dai kawo yanzu fadar shugaban Najeriya ba ta mayar da martani kan rahoton ba, to amma mai magana da yawun gwamnatin jihar Kano da rahoton ya ambato, Malam Aminu Yassar, daraktan yada labarai na cewa ba su san hanyoyin da hukumar ta bi wajen samar da rahoton ba don haka ba za su ce uffan kan sahihancinsa ba.

Amma Yassar din ya ce tabbas an samu rikici nan da can tsakanin matasa a lokacin zaben gwamna da na shugaban kasa da aka yi a jihar, sai dai ya zargi jam'iyyar PDP ta hamayya da tayar da zaune tsaye a wancan lokacin.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment