Friday, 28 June 2019

Alkalin da ya bayar da umarnin kama tsohuwar ministar Jonathan, Diezani ya mutu

Rahotanni sun bayyana cewa, alkalin da ya bayar da umarnin kama tsohuwar ministan mai a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan watau Diezani Alison Maduekwe ya mutu a jiya, Alhamis.The nation ta ruwaito cewa alkali, Valentine Ashi ya mutune bayan da aka garzaya dashi asibi a birnin tarayya, Abuja.

Saidai ba'a bayyana ko wane irin ciwone yayi sanadin mutuwar tashi ba.

Alkalai Valentine Ashi a shekarar 2018 ya bayar da umarnin 'yan sanda da 'yansandan farin kaya su kamo tsohuwar ministar saboda hannu da ake zarginta dashi wajan badakalar batan miliyoyin Naira daga lalitar gwamnati.

No comments:

Post a Comment