Pages

Friday 21 June 2019

Alkawura 30 da shugaba Buhari ya dauka a wa'adin mulkinshi na 2

Cibiyar ’Yan Jarida ta Kasa da Kasa (IPC), ta fitar da bayanai na alkarurran da Shugaba Muhammadu Buhari ya dauka a kamfen din zaben shugaban kasa a 2019.


Cikin jawabin da wannan kungiya ta fitar wanda Jami’in Shirye-shirye, Sanmi Falobi ya sa wa hannu, ya ce Buhari ya yi wadannan alkawurra a lokutannkamfen din sa.

Wadannan alkawurra sun hada dai IPC ta tsakuro su ne daga jaridun The Nation, The Punch, Daily TRUST, Vanguard, This Day, Leadership da kuma Nigerian Tribune.

ALKAWURRA 30 DA BUHARI YA SAKE DAUKA ZABEN 2019

1. Za a dauki wadanda suka kammala digiri su milyan 1 a karkashin N-Ppower, sannan kuma a koya wa wasu milyan 10 sana’o’i a karkashin hadin guiwa da kamfanoni masu zaman kan su.

2. Za a kara yawan daliban da ake ciyarwa daga milyan 9.3 zuwa milyan 15. Za a kara samar wa masu sayar abinci har sub 300,000 ayyukannyi kenan.

3. Za a kammala titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano, wanda aka faro daga Lagos da nufin karasa shi zuwa Kano.

4. Za a kammala titin jirgin kasa daga Fatakwal zuwa Maiduguri.

5. Za a kammala titin jirgin kasa daga Itakpa zuwa Warri ya zarce Abuja ta hanyar Lokoja.

6. Za a kammala aikin gadar Kogin Neja ta biyu da babban titin da ya hade Warri, Jihar Delta zuwa Oron a Jihar Akwa Ibom zai bi ta Kaiama da Fatakwal a jihar Bayelsa da Ribas.

7. Za a kafa Bankin Al’umma mai suna Moni Bank.

8. Za a gina tsarin bayar da lamunin da ya kai naira milyan daya ga kananan ‘yan kasuwa ko ‘yan tireda

9. Za a kara yawan masu cin moriyar Trader Moni, Market Moni da Farmer Moni daga su milyan 2.3 zuwa milyan 10.

10. Za a kara yawan mata a cikin gwamnati, ta yadda yawan su zai kai kashi 35 bisa 100.

11. Za a kara daukar matasa a matsayin hadimai ga ministoci da kuma ta fannin saka su a gurabun wasu nade-nade a hukumomin gwamnati.

12. Za a kirkiro wani shirin cicciba matasan da suka kammala sakandare ta hanyar yin amfani da matasan da aka dauka aiki a karkashin ofishin ministoci da sauran ma’aikatu.

13. Za a sake tsarin manhajar karatu da inganta fasalin tunanin koyo da koyarwa.

14. Za a ci gaba da rike malamai masu koyarwa a makarantun gwamnati na firame da sakandare tare da samar da tsarin amfani da kwamfutoci wajen ilmantarwa.

15. Za a rika gyara makarantu 10,000 tare da saka musu kayan koyarwa na zamani a duk shekara.

16. Za a kammala titina 365 da aka fara a fadin kasar nan.

17. Za a samar da kayan more rayuwar al’umma tare da inganta tattalin arziki.

18. Za a karasa yi wa Boko Haram kwaf-daya tare da kawar da sauran matsalolin tsaro.

19. Za a kawar da cin rashawa da habbaka tattalin arziki.

20. Za a kafa wuraren sarrafa kayayyakin masana’antu a dukkan shiyyoyin kasar nan shida.

21. Za a kafa cibiyon aikin masana’antu na musamman 109 fadin kasar nan, inda za a kafa daya a kowace shiyyar mazabar sanata daya.

22. Za a inganta hanyoyin gaggauta fitarwa da sayar da kayan da ake sarrafawa zuwa kasashen ketare.

23. Za a inganta hanyoyi da dabarun korar fatara da yunwa.

24. Za a tabbatar da an kammala aikin Madatsar Ruwan Samar da Hasken Lantarki da Mambila da Gadar Mambilla.

25. Za a tabbatar da an gina titin jirgin kasa daga Makurdi zuwa Maiduguri.

26. Za a kammala ginin gadoji a yankunan Kogin Benuwai cikin karamar hukumar Ibi.

27. Za a ci gaba da inganta harkokin noma ta hanyar bin matakan bai wa ayyukan gona muhimmanci. Tare da samar da takin zamani a wadace ga manoma.

28. Za a farfado da Masana’antar Karafa ta Ajaokuta.

29. Za a tabbatar da kammala Tashar Hasken Lantarki ta Zungeru.

30. Za a nada mutane sahihai, nagari ba gurbatattu ba a mukaman ministoci.
Premiumtimeshausa.


No comments:

Post a Comment