Saturday, 1 June 2019

Allah ya sake baka dama a karo na 3: Ina fatan A wannan karin abubuwa zasu inganta>>Diyar shugaban kasa, Zahara Buhari ta gayawa mahaifinta

Diyar shugaban kasa, Zahara Buhari ta aikewa da mahaifin nata da sako bayan ya zarce akan kujerar mulkin Najeriya a karo na 3, Daya a mulkin soja, biyu ana dimokradiyya.Zahara ta saka hotunan ranar rantsar da shugaba Buhari tun daga mulkin soja har zuwa na zaben 2019.

Zahara ta rubuta sakon me cike da shauki da kuma ya dauki hankula sosai a shafinta na Instagram inda tace, A karo na 3 Allah ya sake baka dama, ina Addu'ar Allah ya bada ikon yin shugabanci na adalci.

Zahara 'yar shekaru 24 ta ci gana da cewa, a wannan karin ina fatan da addu'ar ganin abbubuwa sun inganta, sannan an biyama 'yan Najeriya bukatunsu daidai gwargwado, sannan masu rike da mukamai su wa 'yan Najeriya aiki tsakani da Allah da kuma girmama su. Allah ya taimake mu.

No comments:

Post a Comment