Pages

Wednesday 26 June 2019

Amosun ya karyata labarin sayen makamai ba bisa izini ba

Hukumar 'yansandan jihar Ogun ta hannun kwamishinan 'yansandan jihar, Basir Makama ta karyata labarin cewa tsohon gwamnan jihar, Ibikunle Amosun ya basu tarin makamai a lokacin da zai ajiye mulki.



Da yake magana da jaridar The Nation, Makama yace basu karbi makamai ba a hannun tsohon gwamnan, ya dai basu albarusai wanda yace sun kai miliyan 4 amma da suka kirga daga baya sun ga cewa duka-duka ba su wuce miliyan daya da dubu dari hudu da 'yan kai ba.

Kwamishinan 'yansandan ya kara da cewa tsohon gwamnan bai basu wasu makamai ba amma dai abinda ya sani shine,makaman da ake magana akansu tun a shekarar 2012 ne gwamnan ya siya ya kuma baiwa  hukumar 'yansanda.

Premiumtimes dai ta ruwaito cewa gwamnan ya baiwa kwamishinan 'yansanda miliyan 4 na albarusai da bindigogin AK47 guda dubu 1 da rigunan da harsashi baya ratsawa guda dubu 1 da kuma motar yaki guda 1.



Rahoton ya kara da cewa tsohon gwamnan ya samu izinin shigowa da makaman sannan kuma an amince mai.

Wani dan sanda da baiso a fadi sunanshi ba ya bayyana cewa, gwamnatocin jihohi sukan yi haka a Najeriya su sayowa 'yan sanda kayan aiki saboda matsalar rashin kayan aikin da suke fama da ita.

Dansandan ya kara da cewa tsohon gwamnan ba kanshi ya siyowa makaman ba, ya ajiyesune a gifan gwamnati saboda idan ya ajesu a hedikwatar 'yansanda, shugaban 'yansandan na kasa ka iya a kowane lokaci bukatar a dauki makaman zuwa wata jiha da take bukatarsu kuma kwamishinan 'yansanda ba zai iya hanashi ba.

Shima gwamnan ya kare kanshi inda yace ya samu izinin shigo da makaman.

No comments:

Post a Comment