Friday, 14 June 2019

An daure tsohon Firaministan Aljeriya saboda almundahanar kudaden gwamnati

An daure tsohon Firaministan Aljeriya Ahmad A-Uyahya da tsohon Ministan Sufuri Abdulgani Zalan a gidan kurkuku bisa samun su da almundahanar kudaden gwamnati.


Tashar talabijin ta Aljeriya ta sanar da cewar bayan Uyahya ya bayar da shaida kan tuhume-tuhumen da ake masa a gaban kotu an yanke masa hukunci tare da aika shi zuwa gidan kurkukun Al-Hirash dake Babban Birnin Kasar.

A labaran da aka fitar an bayyana cewar baya ga Uyahya, an kuma daure tsohon Ministan Sufuri Zalan wanda shi ma bayan ya bayar da tasa shaidar kotu ta tura shi gidan maza.

Zalan shi ne Daraktan kamfe na Shugaba Abdulaziz Buteflika da ya so sake takara a karo na 5 a Aljeriya.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment