Friday, 14 June 2019

An kama dan majalisa kan marin abokiyar aikinsa a Kenya


An kama wani dan majalisar dokokin kasar Kenya Rashid Kassim kan zargin sa da cin zarafin wata abokiyar aikinsa da ya mara, Fatuma Gedi, wacce ke shugabantar kwamitin kasafin kudi.

Ms Gedi ta zargi Mr Kassim da marinta a wajen ajiye motoci na majalisar da ke Nairobi babban birnin kasar, bayan da ya tunkare ta don jin dalilin da ya sa ba ta ware wa mazabarsa ta Gabashin Wajir kudi ba daga cikin kasafin.

Masu amfani da shafin Twitter sun yi ta yada hoton Ms Gedi da jini a bakinta bayan zargin dukan.

Bayan faruwar lamarin ne sai 'yan majalisa mata suka fice daga zauren suna zanga-zanga:

Mista Kassim dai bai ce komai ba dangane da zargin.

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yi ta tur da Allah wadai da Mista Kassim kan yadda ya "ci zarafin mace."
BBChausa.

No comments:

Post a Comment