Saturday, 8 June 2019

An karyata cewar Saudiyya ta yi afuwa ga manyan Malaman Musulunci da za ta kashe bayan Sallar nan

An karyata cewar Masarautar Saudiyya ta yi afuwa ga wasu manyan Malaman Musulunci da suka hada da Selman Al-Awde da za ta zartarwa da hukuncin kisa bayan Sallar nan.


Kungiyar kare hakkokin fursunoni ta Saudiyya ta fitar da wata sanarwa ta shafin Twitter cewar ba gaskiya ba ne batun an yi afuwa ga manyan Malaman, asali ai hakinsu nesu samu 'yanci, ya kamata nan da nan Saudiyya ta saki Malaman.

Har yanzu gwamnatin Saudiyya ba ta ce komai kan wannan batu ba.

Shafin yanar gizo na Middle East Eye ya bayyana cewar a shekarar 2017 aka kama manyan Malaman Musulunci Selman Al-Avde, Hatip Avad Al-Karni da mai gabatar da shirye-shiryen Musulunci a Talabijin Ali Al Umar wadanda bayan Sallar nan za a zartar musu da hkuncin kisa.
TRThausa.


No comments:

Post a Comment