Saturday, 8 June 2019

An 'yantar da fursuna mafi tsufa a Najeriya

Wani fursuna da aka bayyana mafi tsufan shekaru a gidan yarin Najeriya ya samu afuwa bayan shafe shekaru a tsare.


Dattijon da aka bayyana sunan shi Celestine Egbunuche ya shafe shekara 18 a gidan yari bayan yanke masa hukuncin yunkurin yin kisa.

Egbunuche ya hadu da 'yarsa bayan fitowarsa daga gidan yarin Enugu.

Wata kungiya mai zaman kanta ce mai yaki da rashawa ta yi gwagwarmayar ganin an sake shi.

'Yarsa mai suna Chisom Celestine ta shaida wa BBC cewa tana cike da farin ciki. "Muna godiya da wannan rana."

Dattijon ya yi fama da rashin lafiya sosai a gidan yari, inda yake fama da cutar ciwon shuga da matsalar ido.

Yanzu haka yana asibiti ana diba lafiyar shi, yayin da babu tabbas kan ko mai zai iya faruwa da shi nan gaba.
BBCHausa.


No comments:

Post a Comment