Tuesday, 11 June 2019

An yi adalci a zaben kakakin majalisa, zan baiwa Sanata Ahmad Goyon baya>>Sanata Ali Ndume

Sanata Ali Ndume da yayi takarar neman zama kakakin majalisar dattijai wanda Sanata Ahmad Lawal ya lashe zaben ya bayyana cewa an yi zaben bisa Adalci.Sanata Ndume ya bayyana hakane yayin da yake hira da manema labarai bayan kammala zaben inda yace fitowa takarar da yayi yayi ne dan kara tabbatar da kafuwar dimokradiyya.

Ya kara da cewa bashi da matsala da zaben dan an yi shi cikin adalci kuma zai baiwa sanata Ahmad da ya lashe zaben duk goyon bayan da ya kamata dan ganin an samu nasara kamar yanda kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito.

A lokacin da ake zaben mataimakin kakakin majalisar dattijan wanda aka kara tsakanin sanata Ike Ekweremadu da sanata Ovie Omo-Agege, Sanata Udume din ya kauracewa zaben Inda aka yi ta kiran sunan shi dan yazo ya kada kuri'arshi amma bai bayyana ba.

No comments:

Post a Comment