Thursday, 13 June 2019

AN ZABI SARKIN KANO A MATSAYIN SHUGABAN JAMI'AR EKITI

Jami'ar jiha ta Ekiti ta zabi Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a matsayin shugabanta. 


A cikin wata takardar nuna amincewa da aka rubuta wa sakataren gwamnatin jihar Ekiti, Matawallen Kano, Aliyu Ibrahim Ahmad, ya bayyana wa Gwamnan  gamsuwa da jin dadin Sarkin na gano cancantar Malam Muhammadu Sanusi II ta zamowa Shugaban Jami'ar jiha ta Ekiti da suka yi. 

Matawallen Kano ya kara da cewa Mai Martaba Malam Muhammadu Sanusi II zai yi amfani da dukiyarsa, iliminsa da kwarewarsa gurin bunkasuwar jami'ar domin karuwar al'umma.

Idan ba a manta ba, Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusu II shi ne kuma shugaban Jami'ar Benin da ke jihar Edo da kuma Jami'ar Skyline da ke jihar Kano.No comments:

Post a Comment