Tuesday, 11 June 2019

Ba dan inyi nasara na tsaya takarar mataimakin kakakin majalisa ba>>Sanata Ike Ekweremadu

Tsohon mataimakin kakakin majalisar dattijai, Sanata Ike Ekweremadu yayi magana bayan kayen da ya sha a zaben da aka yi tsakaninshi da sanata Ovie Omo-Agege wanda shine sabon mataimakin kakakin majalisar.Sanata Ekweremadu ya bayyana cewa, fitowa takarar da yayi ba wai maganar wa yayi nasara bane ko kuma wa ye be yi nasara ba, ya fito ne a kurarren lokaci kuma dan yayi bayani.

Yace rashin nasarar da yayi damace a gareshi ta samun hutu daga aikin shugabanci wanda ya kwashe sama da shekaru 20 yana yi. Ekweremadu dai shine mataimakin kakakin majalisar dattijai tun daga shekarar 2007 har zuwa 2019.

Ya kara da cewa saidai abinda bai ji dadi ba shine yanda APC ta tsayar da mutumin da ake zargi da hannu wajan satar sandar majalisa a matsayin dan takarar mataimakin kakakin majalisar, yace yayi tsammanin APC zata tsayar da dan takarar da kowa zai amince dashi

No comments:

Post a Comment