Monday, 10 June 2019

Ba ni da shirin ritaya yanzu>>Ronaldo

Cristiano Ronaldo ya ce ba shi da shirin yin ritaya ta gaggawa daga buga wa tawagar kwallon kafar Portugal wasanni.


A ranar Lahadi Portugal ta lashe sabon kofi da aka kirkira na Nations League, bayan da ta yi nasara a kan Netherlands a birnin Porto da ci 1-0.

Ronaldo bai buga wa Portugal wasu wasannin cikin rukuni ba, amma ya taka rawar gani da ta kai kasar wasan karshe, wanda ya ci Switzerland kwallaye uku rigis a wasan daf da karshe ranar Laraba.

Dan kwallon na Juventus na fatan ci gaba da buga wa Portugal wasanni wadda take da matasan 'yan kwallo karkashin Bernardo Silva na Manchester City wanda ya lashe kyautar gwarzon gasar.


Portugal ce ta lashe kofin nahiyar Turai a shekarar 2016, wadda take sa ran kare kambinta a shekara mai zuwa.

Ronaldo ya ce ''matsayar yana nan da koshin lafiya zai ci gaba da wakiltar kasarsa, domin abin da nake alfahari kenan''.

Dan wasan, wanda ya kai shekara 16 yana yi wa tawagar kwallon kafa ta Portugal tamaula, shi ne kadai ya rage daga 'yan kwallon da Girka ta yi nasara a kansu a wasan karshe a gasar kofin nahiyar Turai a 2004.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment