Sunday, 9 June 2019

Babana ya gaya min idan mutum ya taimaki mabukaci, Allah zai nunka mai>>Kalli abinda Ronaldo yawa wani karamin yaro da yace ya rungumeshi

Tauraron dan kwallon kasar Portugal me bugawa kungiyar kwallon kafa ta Juventus wasa, Cristiano Ronaldo wanda ya koma kasarshi inda ya buga wasan kusa dana karshe da suka buga da kasar Switzerland na cin kofin Nations Cup na turai inda har yaci kwallaye 3. Ya kuma yi wani abin daukar hankalin, saidai a wannan karin ba a filin wasa bane.Kungiyar kwallo kafar kasar Porttugal suna atisayen su a garin Porto. Inda bayan sun kammala atisayen sukan koma otal dinsu. Akan hanyar komawa otal dinne sai Ronaldo ya ga wani yaro karami dake fama da cutar kansar jini yana rike da wani kwali inda aka rubuta Cristiano ka rungumeni.

Ai kuwa da ganin wannan yaro, Ronaldo be yi wata-wata ba ya tsaida motar dake dauke dasu inda ya biyawa yaron bukatarshi inda ya rungumeshin. Kalli yanda lamarin ya kasance a kasa:


A baya Ronaldo ya sha nunawa masoyanshi godiya bisa soyayyar da suke nuna mai ta hanyoyi daban-daban kuma yakan bayar da taimako ga mabukata inda a shekaru 4 da suka gabata sai da aka bayyanashi a matsayin mutun na daya a Duniya da yafi kowanne mutum kyauta.

Ronaldo ya taba fadawa ESPN cewa, halin kyautar da yake dashi ya samo asaline daga mahaifinshi dan kuwa ya sha koyamai cewa idan mutun ya taimaki mabukata to Allah zai nunkamai abinda ya bayar.

No comments:

Post a Comment