Friday, 28 June 2019

Barcelona ta dauki Neto daga Valencia

Barcelona ta dauki dan wasan tawagar kwallon kafa ta Brazil, Neto daga Valencia kan kudi fam miliyan 23.3.


Nato mai tsaron raga ya koma Camp Nou, inda zai maye gurbin Jasper Cillessen wanda ya koma Valencia kan Yuro miliyan 35.

Barcelona ta kulla yarjejeniyar shekara shida da mai tsaron ragar mai shekara 29, wadda za ta kare a karshen kakar 2022-23.

Kungiyar ta saka fam miliyan 179 ga duk wadda take son sayen mai tsaron ragar, idan kwantiraginsa bai kare a Nou Camp ba.

Neto ya buga wa Valencia wasa 47 a kakar da aka kammala, inda ya yi karawa 10 kwallo bai shiga ragarsa ba.

Golan ya taimaka wa Valencia ta kare a mataki na hudu a teburin La Liga, hakan na nufin kungiyar za ta buga Champions League a bana.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment