Saturday, 22 June 2019

Barcelona ta gindayawa Neymar sharuda 3 kamin ta sake sayenshi kuma duk ya amince: Sharadi na 3 zai sa ka rike baki

Rahotanni dai na kara dumama akan barin PSG zuwa Barcelona da Neymar ke kokarin yi inda a yanzu wasu rahotannin da zafizafinsu ke bayyana cewa Barca ta gindayawa Neymar sharudda 3 kuma ya amince dasu kamin ta yadda ta sake dawo dashi.Dama dai tuni PSG ta budewa Neymar hanya akan barin kungiyar inda aka ji shugaban kungiyar, Nasser Al-Khelifi na fadin cewa babu wanda ya tirsasawa Neymar din zuwa PSG da kanshi ya amince ya zo ya buga musu wasa kuma su a shirye suke duk wanda yaga ba zai iya mayar da hankali dan musu wasan daya kamata ba ya kama gabanshi.

Rahoton wata kafar watsa labarai ta Brazil me suna, UOL Esporte yace, Barcelona ta gindayawa Neymar sharuddan kamar haka:

Dole ya hakura da kudin shi na sallama da yake ta kokarin su biyashi. A lokacin da Neymar ya koma bugawa PSG wasa, akwai kudin da ya kamata Barcelonar su biyashi da yake ta bibiya amma har yanzu basu bashi ba, sune sukace ya hakura dasu. Kuma ya amince.

Dole Neymar ya bayyanawa Duniya cewa barin Barcelona da yayi kuskurene kuma a yanzu ya gane kurenshi shiyasa zai dawo.

Kasancewar Barcelona bata kai PSG karfin tattalin arziki ba, ta bukaci Neymar ya yadda ta rage mai Albashi, kuma ya yadda da hakan.


No comments:

Post a Comment