Thursday, 13 June 2019

Bude gidan rawa a Saudiyya ya jawo ce-ce-ku-ce


Batun bude wani gidan rawa na halal a birnin Jiddah na kasar Saudiyya ya mamaye shafukan sada zumunta na kasar, inda mutane da dama ke bayyana ra'ayoyinsu kan hakan.

Wani gidan rawa na birnbin Dubai a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa mai suna White ne ya sanar da bude sabon gidan rawar da ya kira "Halal Disco" a Jiddah a ranar Alhamis.

Kafofin yada labarai na kasar sun tabbatar da bude gidan rawar wanda suka ce tsarinsa ya yi kama sosai da gidan casu na dare da aka sani, sai dai kuma ba za a dinga shan barasa a wajen ba.

Shi ma gidan rawar na White ya ce wurin zai yi kama ne da dakin hira ba da mashaya ba.

Wasu rahotannin sun kuma ce mata ba za su sanya abaya ba, amma mamallakan wajen sun ce yanayin suturar da za a dinga sa wa za ta zama sassauka.

Ana ganin wannan lamari dai a matsayin irin sauye-sauyen da ake yi a bangaren nishadantarwa na kasar a karkashin jagorancin Yarima mai Jiran Gado Mohammed bn Salman.

An yi ta yada wasu hotunan bidiyo a intanet da ake ikirarin cewa daga gidan rawar ne, wadanda ke nuna filin casun da fitilu.

Wannan batu dai ya raba kan 'yan kasar biyu inda wasu suka tunzura da labarin tare da yin Allah-wadai da matakin gwamnati na ba da damar bude gidan rawar a kasar, wacce suke ganin tana kare kimarta tsawon gomman shekaru.

Amma a daya bangaren wasu murna suke da samun gidan rawar, irinsa na farko a kasar.

An yi ta kuma yada wasu hotunan masu kamar shagube ga lamarin:
An kaddamar da maudu'an "#ديسكو_في_جده" Disco in Jeddah da kuma na #بار_حلال "Bara Halal" a shafin Twitter a kasar, inda cikin sa'o'i kadan suka yadu kamar wutar daji.

An yi amfani da maudu'an sau fiye da 70,000, kuma mafi yawan wadanda suka yi amfani da su masu goyon bayan lamarin ne.

A hannu guda kuma masu sukar batun su ma sun kirkiri wani maudu'in #لاارضي_بمنكرات_شاطي_بيتش_بجده "Ban yarda da abubuwa marasa kyau ba a Jedda, wanda shi kuma aka yi ta amfani da shi kusan sau 4,000.

Masu sukar lamarin dai suna ta kira ga hukumomin kasar da kar su bari a bude gidan rawar na dare, suna masu cewa ya kamata a kare tare da tsare kyawawan al'adu na kasar.

Wani mai amfani da Twitter @miso8m ya rubuta cewa: "Gidan rawa a Jiddah? Wannan ne lokacin da mumini zai so a ce ya mutu da ya ga irin wannan lamari."
BBChausa.

No comments:

Post a Comment