Sunday, 2 June 2019

Buhari ya goyi bayan tabbatar da 'yancin Falasdinawa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari goyi bayan kudirin kungiyar kasashen musulmi OIC na tabbatar da samun 'yancin Falasdinawa.


Shugaban ya fadi haka ne lokacin da yake karanta jawabi a madadin mambobin kungiyar na kasashen Afirka a wajen babban taron da aka gudanar a Makkah kasar Saudiyya.

A cikin jawabin ya ce, kasashen Afirka sun yaba da kokarin kungiyar OIC na tabbatar da 'yancin Falasdinawa da kuma kawon karshen rikicin gabas ta tsakiya da aka shafe shekaru ana yi.

Shugaban ya ce mambobin kasashen na fama da barazanar tsaro, da suka hada da ta'addanci da tsauttsauran ra'ayi da kuma rikicin 'yan bindiga.

Ya ce matsaloli ne da suka dade ana fama da su wadanda suke bukatar daukar matakan kawo karshensu gaba daya.

Ya yaba da ayyukan OIC na shawo kan rikicin kasasahen Syria da Yemen da Libya da kuma rikicin musulmin Roginya tsiraru a Myanmar.

Shugaban ya ce kungiyar tana tasiri sosai ga Najeriya da sauran kasashen Afirka, musamman Bankin Musulunci IDB da ke tallafi a fannin kasuwanci da noma da fasaha da yaki da talauci tsakannin mata da matasan Afirka.

Sannan ya ce kungiyar na bada taimako ga yaki da ta'addanci a kasashen yammcin Afirka da na tafkin Chadi da kuma Sahel.

Shugaban Saudiya Sarki Salman Bin Abdul Aziz Al-Saud ya jagoranci taron, inda kuma shugaba Recep Erdogan na Turkiya ya kawo karshen wa'adin shugabancinsa na kungiyar.
BBChausa.


No comments:

Post a Comment