Friday, 7 June 2019

Buhari ya soma Sulhunta Rikicin Ganduje da Sarki Sanusi

Daga karshe dai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yanke shawarar shiga tsakanin rikicin da ke ruruwa tsakanin gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da Mai Martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II. 


A 'yan kwanakin nan ne mutane da dama da suka damu da jihar Kano suka yi ta yin kiranye-kiranye ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran dattawan Arewa da su shiga tsakanin rikicin da ke tsakanin wadannan manyan shuwagabannin jihar domin samun kwanciyar hankali da ci gaban jihar.

Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa majiyarmu ta DAILY NIGERIAN cewa Shugaban kasar ba ya farin ciki da abin da ke wakana a jihar, sakamakon yadda ake ta Allah-wadai da nuna takaici a kan abin da ke wakana a babbar jihar.

"Kun san shugaban kasa bai cika yin katsalandan a cikin sha'anin jihohi ba. Amma a game da wannan batun, dole dai ya shiga tsakani," majiyar ta fada. 

"Shugaban kasa ba ya farin ciki da gwamnan sakamakon yanke shawarar da ya yi mara farin jini ta kakkarya masarautar tare da yunkurin tsige sarkin." 

"Hakan ya sanya shugaban kasa ya yi sammacin Ganduje a ranar Alhamis tare da umartar shugaban hukumar DSS da ya kira mitin din gaggawa da gwamnonin arewa maso yamma. 

"Gwamnonin sun sami jagorancin gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, wanda tun da fari ya hadu da shugaban kasa, ya yi masa jawabi game da batun." 

Majiyarmu ta DAILY NIGERIAN ta kuma bayyana cewa shi ma Mai Martaba Sarkin Kano an yi sammacin sa da Madakin Kano, Yusuf Nabahani, a ranar Juma'a.
Sarauniya.


No comments:

Post a Comment