Saturday, 1 June 2019

Chelsea na Neman Coutinho ya maye mata Hazard

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea na neman Philippe Coutinho na Barcelona dan ya maye mata gurbin dan wasanta Eden Hazard da zai koma Real Madrid da wasa.Mail ta ruwaito cewa Chelsea na mafarkin hakanne idan ta samu nasara aka dage mata dakatarwar da aka mata na sayen 'yan wasa.

Barcelona dai na neman Yuro miliyan 150 ne akan Coutinho kuma masu sharhi na ganin cewa zai fi wa dan wasan Alheri idan ya bar Barca musamman ganin cewa me horas da 'yan wasan kungiyar baya yi dashi.

No comments:

Post a Comment