Thursday, 6 June 2019

DA DUMI-DUMI: GANDUJE YA AIKA DA SARKIN KANO TAKARDAR TUHUMA

Gwamnatin jihar Kano ta aikawa da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II takardar tuhuma, ya kuma nemi ya kare kansa cikin awa 24.


Jaridar Prime Time News ta ruwaito cewa, an aikewa Sarkin tuhumar ne sakamakon zarginsa da barnatar da Kudin Masarautar Kano kimanin Naira Biliyan 3.4.

A cewar jaridar ana tsammanin Sarkin ya kare kansa daga wannan zargi kafin a kai ga dakatar da shi. 

Daga Masarautar kuwa tuni suka karyata wannan batu ta hanyar fitar da takarda ga manema labarai.

Rahotanni na cewa a kowane lokaci daga yanzu gwamnati za ta iya bayar da sanarwar dakatar da Sarkin.
Sarauniya.


No comments:

Post a Comment