Tuesday, 4 June 2019

Dan Najeriya daga jihar Sakkwato ya zama shugaban majalisar dinkin Duniya

Farfesa Tijjani Muhammad Bande, tsohon mataimakin shugaban jami'ar Usman Danfodiyo dake Sakkwato ya zama shugaban majalisar Dinkin Duniya.A yau aka yi zabe a hedikwatar majalisar dake birnin New York inda aka zabi farfesa Tijjani a matsayin shugaban majalisar wanda kuma dama shi kadaine ya tsaya takara. Shine dan Najeriya na biyu da ya rike wannan mukami bayan Joseph Garba wanda tsohon sojane kuma wakilin Najeriya a majalisar wanda yayi shugaban ci daga shekarun 1989 zuwa 1990. A watan Satumba ne za'a rantsar dashi.

No comments:

Post a Comment