Wednesday, 12 June 2019

Duk Wanda yasa hannu a dokar yin wa'azi yayi ridda>>Dr. Ahmad Gumi

A kwanakinnan ne majalisar jihar Kaduna ta amince da dokar sanya ido akan yanda ake wa'azi a jihar dokar da gwamnan jihar ya dade yana bukatar majalisar ta amince mai dan aiwatarwa.Dokar ta jawo cece inda tun da farko ake ganin dalilin jan kafa wajan kin amincewa da dokar shine gudun abinda zai je ya dawo da 'yan majalisar ke yi.

Amincewa da dokar ya samu yabo daga wasu al'ummar jihar yayin da wasu suka yi Allah wadai da ita.

Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana ra'ayinshi akan wannan sabuwar doka kamar yanda Rariya ta ruwaito inda yace, 'Duk Wanda Ya Sa Hannu A Dokar Yin Wa'azi Ya Yi Ridda, Cewar Sheik Dakta Ahmad Gumi'

No comments:

Post a Comment