Sunday, 30 June 2019

EFCC zata gurfanar da Saraki a gaban kotu bisa zargin Almundahanar kudi

Hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC a takaice zata gurfanar da tsohon kakakin majalisar dattijai, Bukola Saraki bisa zargin almundahanar kudaden da suka kai Naira biliyan 12.EFCC ta ce Saraki ya karkatar da wadancan makudan kudi ne lokacin yana gwamnan Kwara inda ya rika cirar Naira Miliyan 100 duk wata daga lalitar gwamnatin jihar dan sayen wasu gidaje a birnin Legas.


No comments:

Post a Comment