Saturday, 1 June 2019

FA'IDODIN DAKE CIKIN YIN AURE

Fa'idodin da suke cikin aure ba za su kididdigu ba. Amma ga wasu kadan daga ciki za mu lissafo kamar haka:

1. Yin aure biyayya ne ga umurnin Allah da Manzonsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam). 

2. Yin aure yana sanya Manzon Allah (SAW) farin ciki a ranar lahira. Yace : "Ku yi aure ku hayayyafa. Domin ni zan yi ma sauran al'ummomi alfahari da ku a ranar alkiyama".

3. Ta dalilin aure za ka samu wanda zai fito ta jikinka, har ya girma yana Kalmar Shahada!! "LA ILAHA ILLAL LAHU MUHAMMADUR RASULALLAHI. 

4. Ta dalilin aure ne za ka samu zuriyar da za su yi maka addu'a bayan rasuwarka.  Wannan yana daga cikin ayyukan da ladansu ba zai yanke ba har abada. 

5. Yin aure ya kan zama dalilin runtsewar idanun mutum daga kalle kallen haramun, sannan ya kare masa al'aurarsa daga zina. 

6. Ta dalilin aure ne za ka samu damar taimakawa 'yar uwarka Musulma, ka aureta, ka Kiyayeta kenan daga zina. 

7. Ta dalilin aure ne zaka samu cikar addininka, da ninkawar ladanka fiye da wanda bashi da aure. 

8. Ta dalilin aure ne zaka samu ladan ciyarwa da Matarka, da daukar nauyinta, da ladan samar mata da Mazaunin da zata rayu. 

9. Ta dalilin aure ne zaka samu damar Qara yawan Musulman duniya ta hanyar haihuwar da zaka samu. 

10. Ta dalilin aure ne zaka samu damar Karkatar da himmarka daga kan neman biyan bukatarka ta hanyar haram izuwa ga hanyar halal. Da kuma samun ladan saduwa da iyalanka. 

11. Zaka samu lada mai girma sosai idan Har Allah ya azurtaka da 'Ya'ya mata guda biyu, kumq kayi hakuri dasu ka kyautata musu, ka kyautata tarbiyyarsu, Su zasu zama Garkuwarka daga shiga wuta. 

12. Idan kuma har 'Ya'yanka guda biyu suka rasu, kuma kayi hakuri, to Allah zai shigar dakai Aljannah saboda wannan. 

13. Ta dalilin aure zaka samu karuwar mutuncinka da darajarka acikin al'ummah. Ka shiga sahun mutanen da zasu iya jagorantar lamuran rayuwar al'ummah. 

14. Ta dalilin aure ne za ka samu taimakon Allah cikin al'amarinka. Kamar yadda Manzon Allah (saww) yake cewa: "MUTUM UKU, HAKKI NE AKAN ALLAH YA TAIMAKESU

(a)  WANDA ZAI YI AURE DON NUFIN KAME MUTUNCINSA. 

(b). BAWA WANDA YAKE NEMAN 'YANCINSA SABODA YA SAMU DAIDAITUWA (ACIKIN ADDINI) 

(c). MUJAHIDI (MAI YAKI DON DAUKAKA ADDININ ALLAH).

15. Ta dalilin aure ne zaka samu Qaruwar yawan dangi. Domin duk mutanen da ka auri 'yarsu ko Qanwarsu, to ka zama nasu. 

16. Ta dalilin aure ne zaka samu zuriyya tsarkaka wadanda zasu bauta ma Allah kuma za'a baka ladan dukkan aikin ibadar da sukayi. 

*Muna kira ga Matasan da suke da ikon yin aure, lallai aje ayi aure. arage burin duniya. Kullum rayuwa tafiya take yi.

Daga Malam Umar Sani Fagge

No comments:

Post a Comment