Friday, 7 June 2019

Ganduje yawa Sarkin Kano daurin talala iya masarautar Kano

Wasu rahotanni sun bayyana cewa gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje yawa sarkin Kano, Muhammad Sanusi daurin talala inda ya takaita zirga-zirgar sarkin a iya fadar masarautar Kanon.The Guardian ta ruwaito cewa bayan bukatar ba'asin yanda masarautar ta kashe kudi har Naira biliyan 4 da gwamnatin jihar ta bukata, hakanan gwamnatin jihar ta takaita zirga-zirgar sarkin Kanon a iya fadar Kanon.

Rashin jituwar masarautar Kano da gwamnatin jihar ya fara ne dalilin zargi sarkin Kanon, Muhammad Sanusi da shiga harkar siyasa.

No comments:

Post a Comment