Friday, 7 June 2019

Ganin tsohon gwamnan Zamfara a taron da shugaba Buhari yayi da gwamnoni ya jawo cece-kuce

Ganin tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari a wajan ganawar da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi da gwamnonin Najeriya 36 ya dauki hankula inda wasu suka rika tambayar ko me ya kaishi wajan?.



Saidai wani me sharhi akan al'amuran yau da kullun, ya bayyana cewa:

Game da Batun Zuwan Tsohon Gwamnan Zamfara Abdul'aziz Yari Fadar Shugaban kasa Taron Gwamnoni

Kasancewar kacokam Ganawar da Shugaba Buhari yayi da Gwamnoni 36 na kasar nan ta shafi Mas'alar tsaro ne, wannan tasa aka gayyaci tsohon gwamna Yari na zamfara, da tsohon Gwamnan jihar Borno Kashim shettima da kuma tsohon Gwamnan Jihar Yobe Gaiedam domin su Bayar da wasu Bayanai na Musamman akan tsaron Jihohin.

A Takaice dai Tsoffin Gwamnoni uku ne suka amsa Gayyatar ta Shugaban kasa, wadda tasa aka gansu tare da Sabbin Gwamnoni, kuma idan aka yi duba duka za'a ga Tsaffin Gwamnonin jihohi ne da suke fama da Matsalar Tsaro.

Daga Magaji Ontop Daura

No comments:

Post a Comment